25 Oktoba 2016 - 15:51
Hukumar EFCC Ta Cafke Tsohon Kakakin Shugaban Kasa Reuben Abati

Hukumar yaki da cin hanci da rahawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta ce tana binciken tsohon kakakin shugaban kasa Reuben Abati, bisa zarginsa da hannu a wasu ayyukan na cin hanci da rashawa.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ne ya sanar da hakan, inda ya ce Abati wanda shi ne kakakin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ana zarginsa ne da karbar kudade daga Sambo Dasuki, wadanda aka ware domin sayen makamai a lokacin.

Wilson ya ce Abati zai ci gaba da kasancewa karkashin binciken hukumar har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Hukumar EFCC dai ta ce ta samu Sambo Dasuki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da yin watanda da kudaden sayen makami da suka kai dalar Amurka biliyan biyu.288