11 Oktoba 2014 - 15:19
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar Ebola ta ci rayukan mutane fiye da 4000

Hukumar Lafiya ta kasa da kasa ta bayyana cewa; Adadin wadanda su ka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar Ebola sun haura 4000.

 A wani bayani da kungiyar ta fitar ta ce; A tsakanin adadin mutane 8,399 da su ka kamu da cutar, wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 4,033 ya zuwa ranar 8 ga watan Oktoba. Karuwar masu mutuwar saboda cutar ta Ebola ya zo ne bayan da hukumar lafiyar ta kasa da kasa ta sanar da cewa an sami koma baya matuka a taimakon da ake bayarwa na fada da ita. Baya ga kasashen yammacin Afirka da cutar da fi watsuwa, an sami bullarta a cikin kasashen Amurka da kuma Spain. Gwamnatin Kasar Canada ta shawarci ‘yan kasarta da su kauracewa zuwa kasashen yammacin Afirka da cutar ta yi kamari. ABNA