29 Agusta 2014 - 17:25
Iran Za Ta Ci Gaba Da Taimakawa Palastinawa

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja’afari ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu da kuma taimaka musu da dukkanin abin da suke bukata wajen fada da HKI.

Manjo Janar Ja’afari ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya fitar a yau Juma’ar nan inda ya ce tsayin dakan da al’ummar Gaza suka yi a yayin yakin kwanaki 51 da HKI ta kaddamar a Gazan wani mafari ne na kawo karshen haramtacciyar kasar yahudawan na sahyoniya.

 

Janar Ja’afari ya kara da cewa, baya ga Zirin na Gaza, wajibi ne a karfafa ‘yan gwagwarmayar Palastinawa da suke Yammaci Kogin Jordan don su ma su sami karfin tsayin dakan tinkarar HKI.

 

Sakon na kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar Gazan suke ci gaba da gudanar da bukukuwan samun nasara a kan HKI bayan ta amince da wasu daga cikin sharuddan da suka kafa mata na tsagaita wuta. Ko a yau ma dubun dubatan magoya bayan kungiyar Jihadi Islami ne suka gudanar da wani gangami a Zirin na Gaza don nuna godiya da kuma murnarsu ga wannan nasara da suka samu. ABNA