27 Yuli 2014 - 18:32
Anyi jana'izar Shahidai 17 cikin 33 da aka samo a waki'ar Ranar Qudus

A ranar asabar 28 ga watan Ramadan 1435 ne jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaquob El-Zakzaky ya jagoranci sallar jana'izar Shahidai 17 daga cikin jumlar Shahidai 33 da Allah ya azurta mu da su sakamakon budewa muzaharar Ranar Qudus wuta da sojoji sukayi

Ya zuwa lokacin da aka gabatar da sallar jana'izar a ranar Asabar gawawwaki 17 kawai daga cikin jumlar gawawwakin shahidai 33 suka zo hannu, saboda haka nan su kadai ne aka sallata

Bayan an kammala sallar ne kuma aka dauki Shahidan zuwa makwancin su a Jannatur Rahmah dake can garin Dembo. ABNA