Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tulkarm da sansanonin sa na tsawon watanni kusan uku a ci gaba da fafatawa a fili tare da kaddamar da hare-hare da gargadin ruguza gidajen Palastinawa. A cikin sa'o'i 24 da suka gabata 'yan mamaya na yahudawan sahyuniya sun ba da umarnin rusa gidaje da gine-gine 106 na Palasdinawa a sansanonin 'yan gudun hijira na Tulkarm da Nur Shams.

4 Mayu 2025 - 18:16
Source: ABNA24

Your Comment

You are replying to: .
captcha