16 Yuli 2026 - 15:39
Source: ABNA24
Iraqi: Mummunan Hatsari A Hanyar Tafiya Ta Arba'in Yayi Sanadin Mutuwar Mutane 8

Biyo bayan wani mummunan hatsari da ya faru a hanyar tafiyar tattakin Arba'in a Basra, maziyarta 'yan Iraki 8 sun mutu mutane 17 suka jikkata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Biyo bayan wani hatsarin mota a hanyar tafiyar mahajjatan Arba'in na Iraki a gundumar Hartha, a arewacin lardin Basra na Iraki, mahajjata 8 sun rasa rayukansu kuma wasu 17 suka jikkata.

Hukumar 'yan sandan zirga-zirga ta Basra da safiyar yau Alhamis ta sanar da cewa, wata mota mai ƙarfi nau'in GMC, yayin da take tafiya a kan hanyar da aka keɓe ga maziyarta a unguwar Al-Murtaza ta gundumar Hartha, ta fice daga kan hanyarta ta shiga hanyar tafiyar maziyarta, inda ta yi gaba da wasu daga cikinsu, wanda hakan ya haifar da wannan mummunan hatsari.

Dangane da sanarwar wannan hukuma, an kama direban motar bayan hatsarin, kuma ana ci gaba da bincike game da dalilin hatsarin.

………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha