Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Ahmad Sharif Chaudhry, mai magana da yawun sojojin Pakistan, a ranar Alhamis (17 ga Yuli) a taron manema labarai ya sanar da cewa, biyo bayan hare-hare uku na manyan 'yan tawaye a jihar Balochistan cikin kwanaki hudu da suka gabata, an kashe jami'an tsaro 42 da suka hada da 'yan sanda 27, sojoji 11 da fararen hula 4.
Waɗannan hare-haren sun haɗa da kwanton bauna da ƙungiyar 'Yancin Balochistan (BLA) ta yi wa ayarin sojoji kusa da Bela-Winder (inda sojoji 11 suka mutu), harin da aka kai wa ofishin 'yan sanda a Ziarat, da arangama a yankin Hana Orak na Quetta.
Mai magana da yawun sojojin Pakistan ya kira waɗannan hare-haren a matsayin "ta'addanci," kuma ya yi iƙirarin cewa suna samun tallafi da goyon baya da masu tsara su daga waje, musamman Indiya da ƙasar Afganistan,; zargi da Islamabad ke yawan yi.
Chaudhry, tare da kiran gwamnatin Afganistan a matsayin "gwamnatin Taliban ta Afganistan ba haalastacciya ba," ya yi iƙirarin cewa ƙasar Afganistan ta zama mafaka ga ƙungiyoyin ta'addanci, kuma ya buƙaci a ɗauki mataki a kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Yana mai jaddada cewa Pakistan ba za ta ƙyale a yi amfani da ƙasar Afganistan a kanta ba, ya kara da cewa sojojin Pakistan a wasu ayyukan ramuwar gayya sun kashe 'yan tawaye 54.
Waɗannan abubuwan suna nuna ƙaruwar tashin hankali a Balochistan, inda ƙungiyoyin 'yan awaren Baloch da Tahrik-e-Taliban Pakistan ke aiki.
Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin dukkan hare-haren gaba ɗaya, kuma Taliban na Afganistan ba su mayar da martani ga waɗannan maganganun ba.
.....................
Your Comment