9 Yuli 2026 - 10:19
Source: ABNA24
Amurka Ta Kai Hari Kan Wasu Cibiyoyin Soji Da Hare-Harenta Sau Biyu A Bushehr

A daren jiya, wani sansanin soji a kudancin birnin Bushehr ya fuskanci hare-hare sau biyu na na ta’addancin Amurka.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Jahaniyan, mataimakin gwamnan lardin Bushehr kan harkokin siyasa da tsaro ya ce: Da safiyar ranar Laraba, wani sansanin soji a gundumar Dashti, haka kuma da karfe 9 na safe wani sansanin soji a kusa da garin Choghadek, da kafin la'asarin wannan rana sansanin sojin sama na Bushehr, sun fuskanci hare-haren makiya, wanda ya kai ga shahadar daya daga cikin ma'aikatan sansanin sojin sama mai suna Kyaftin Ali Mu'ini.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha