9 Yuli 2026 - 00:14
Source: ABNA24
Iran: An Samu Canjin Lokacin Jana'izar Shahidin Jagora A Mashhad

Bisa sanarwar kwamitin bankwana da jana'izar jagora shahidi a Mashhad, za a gudanar da jana'izar gawar jagora shahidin juyin juya hali a Mashhad da karfe 2 na rana.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: An fitar da sanarwa mai lamba uku ta kwamitin banwana da jana'izar Shahidin Iran a Mashhad mai tsarki.

Saboda gagarumar tarya da ba a taɓa yin irinsa ba da kuma girmamawa daga al'ummar Iraki, musamman a Najaf Ashraf da Karbala mai tsarki, ga gawar Imam Mujahidi Shahidi, lokacin isowar gawarwakin zuwa Mashhad mai tsarki ya sami jinkiri.

A kan haka, za a gudanar da taron maraba da jana'izar da karfe 14:00 na ranar Alhamis 9 ga Yuli, daga titin Imam Raza (A.S) zuwa haramin Imam Ridha mai tsarki As.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha