Mashhad
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Halartar 'Yan Afganistan A Mashhad A Wajen Jana'izar Shahidin Jagora
Baƙi 'yan Afganistan da ke zaune a Mashhad da sauran wadanda suka shigo kasar Iran domin jana’izar Shahidin Jagora, tare da dinbin halartarsu a jana'izar Shahidin Jagoran juyin juya hali da kuma kafa tantinan hidima a wannan taron tarihi, sun sake yin shela da babbar murya game da soyayyarsu ga jagora masoyi na juyin juya hali, amincinsu ga Jamhuriyar Musulunci, da kuma hadin kai da al'ummar Iran, suna masu tabbatar da hakan a aikace. ............
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Halartar Masu Makoki Wajen Ziyarar Kabarin Jagora Shahidin Juyin Juya Hali A Rukn Darul-Dhikr
Bayan gudanar da binne gawar Ayatullahil-Uzma Shahid Sayyid Ali Khamene'i da shahidan iyalinsa a Rukn Darul-Dhikr na haramin Imam Raza (A.S), tun daga yammacin yau Juma'a (19 ga Ter, 1405 na hijira shamsi), masu makoki Sun sami damar ziyara, kuma taron masoya "Shahidin Iran" sun halarci don ziyarar kabarin jagora shahidin juyin juya hali a Rukn Daril-Dhikr.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Rakiyar Jana'izar Gawar Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Mashhad Mai Tsarki - 2
An gudanar da gagarumar rakiyar jana'izar ga gawar jagora shahidin juyin juya hali da iyalinsa tare da halartar miliyoyin jama'a masu shauki da kishin juyin juya hali na Iran Musulunci a birnin Mashhad mai tsarki.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Rakiyar Jana'izar Gawar Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Mashhad Mai Tsarki - 1
An gudanar da gagarumar rakiyar jana'izar ga gawar jagora shahidin juyin juya hali da iyalinsa tare da halartar miliyoyin jama'a masu shauki da kishin juyin juya hali na Iran Musulunci a birnin Mashhad mai tsarki.
-
An Gudanar Da Sallar Janaza Ga Gawa Mai Tsarki Ta Shahidin Jagora A Haramin Imam Ridha As
Bayan jana'izar gagarumi na gawar jagora shahidin juyin juya halin Musulunci a Tehran, Qom, Najaf Ashraf da Karbala mai tsarki, a yau bayan yin sallah za a gudanar da jana'izar da binne gawar Shahidin Iran a Mashhad mai tsarki da haramin Raza mai tsarki.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Sheikh Zakzaky (H) Ya Isa Birnin Mashhad
Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sauka birnin Mashhad, Jamhuriyar Musulunci ta Iran, don halartar jana'izar Al-Shaheed Imam Khamene'i (QS). Daga Najaf Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya biyo ayarin da suka dauko Imam Al-Shaheed (QS) da za'a bizne a Haramin Imam Reza (AS). Szakzakyoffice 09/07/2026
-
Daruruwan Dubban Al’umma Ne Ke Kwarara Zuwa Kabarin Imam Ridha (A.S) A Mashhad Don Bankwana Da Imam Khamene'i
Taro mai yawa na masu jana'iza da 'yan ƙasa suna tururwa da taruwa a kabarin Imam Ali Ridha (A.S) a birnin Mashhad na Iran, tun daga farkon sa'o'in safiyar yau Alhamis, suna jiran fara jana'izar da bankwana da gawar shugaba shahidin al'umma Sayyid Ali Khamene'i a mahallinsa na ƙarshe, bayan tafiyar jana'izar mai girma da ta ɗauki kwanaki shida ta ratsa Iran da Iraki, inda miliyoyin masu jana'iza ke ɗaga jajayen tutoci don nuna fushi da neman fansa.
-
Rahoto Cikin Bidiyo | Yadda Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Halarci Jana'izar Imam Shahidi A Mashhad
Rahoto Cikin Bidiyo | Yadda Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Halarci Jana'izar Imam Shahidi A Mashhad
-
Rahoto Cikin Hotuna | Yadda Al'umma Ke Jiran Zuwan Isowar Jagora Daga Iraqi A Mashhad
Rahoto Cikin Hotuna | Yadda Al'umma Ke Jiran Zuwan Isowar Jagora Daga Iraqi Zuwa Mashhad
-
Iran: An Samu Canjin Lokacin Jana'izar Shahidin Jagora A Mashhad
Bisa sanarwar kwamitin bankwana da jana'izar jagora shahidi a Mashhad, za a gudanar da jana'izar gawar jagora shahidin juyin juya hali a Mashhad da karfe 2 na rana.
-
Sheikh Zakzaky Ya Shigo Najaf Domin Jana'izar Shahidin Jagora Al'umma + Hotuna
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigo Najaf Ashraf don halartar jana'izar gawar Shahidin Jagoran al'umma. An shirya cewa bayan ganawa da tattauna da malamai da shugabannin addinai na Iraki, zai tafi Mashhad mai tsarki don halartar taron binnewa.