7 Yuli 2026 - 18:01
Source: ABNA24
An Gudanar Da Jana'izar Alamtawa Ga Shahidin Al’umma A Jihar Bauchi, Najeriya + Hatuna

A daidai lokacin da ake gudanar da jana'izar gawar jagora shahidin juyin juya halin Musulunci da iyalinsa a Iran da Iraki, wasu gungun mambobin Harkar Musulunci ta Najeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky, sun gudanar da jana'izar alamci da rakiyar shugaba mai girma na Musulunci a jihar Bauchi, Najeriya.

Bisa Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA - Wasu gungun 'yan Shi'a na jihar Bauchi, Najeriya, yayin da suka halarci hussainiyar Muhammad Bauchi a wannan yanki sun gudanar da ayyukan addini na lokutan makoki na Aba Abdillahil-Husain (A.S), sun yi jana'izar alamtawa da rakiyar gawar Jagora shahidin Iran Ayatullahil-Uzma Imam Khamene'i da iyalinsa masu daraja.

A wannan taron, Sheikh Ahmad Bauchi, ɗaya daga cikin jagogorin harkarr Musulunci ta Najeriya kuma ɗaya daga cikin masu wa'azi na addini a yankin, ya yi jawabi da waƙoƙin juyayi.

Ya kamata a lura cewa, jihar Bauchi yanki ne mai cike da dausayi da koren yanayi da albarka da ke arewa maso gabashin Najeriya, wanda mafi yawan mazaunanta Musulmai 'yan Ahlus-Sunnah ne, kuma a 'yan shekarun baya, da ƙoƙarin harkar Musulunci ta Najeriya, 'yan Shi'a ma sun sami matsayi mai kyau a wannan yanki.

............

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha