4 Yuli 2026 - 22:47
Source: ABNA24
Iraki: Ta Ƙaddamar da Jiragen Kasa Na Musamman A Kan Hanyar Basra - Karbala Domin Jana'izar Shahidin Jagora

Kamfanin Jirgin Kasa na Iraki ya keɓe jiragen kasa na musamman don jigilar masu makoki na jana'izar Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'I Rh a Iraki.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Hukumar Jirgin Kasa ta yankin kudancin Iraki ta sanar da cewa, tare da amincewar babban manajan kamfanin jirgin kasa na wannan ƙasa, jiragen kasa na musamman za su fara tafiya don jigilar fasinjoji daga lardin Basra zuwa birnin Karbala a ranar Talata 7 ga Yuli, shekara 2026.

"Redha Muhammad al-Hashimi" manajan jirgin kasa na yankin kudancin Iraki a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa an keɓe waɗannan jiragen kasa na musamman don jigilar masu makoki don halartar jana'izar Shahid Ayatullahil-Uzma Imam Sayyid Ali Khamene'i a garuruwan Najaf da Karbala.

Ya kara da cewa waɗannan jiragen za su fara tafiya da karfe 20:30 (karfe takwas da rabi na dare).

…………………………..

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha