Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: jaridar yahudawa Yedioth Ahronoth ta ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun rasa "wayar soji ta sirri" a yayin wani aiki a lardin Dara'a na kudancin Siriya, wanda ke dauke da bayanai masu muhimmanci da sirri.
A cewar rahoton, wannan lamari ya faru ne a ƙauyen Abidin na Dara'a, inda aka yi artabu tsakanin sojojin Isra'ila da mazauna yankin. An fara artabun ne da harbin bindiga a wani sansanin soji, bayan haka aka yi amfani da manyan bindigogi da rokoki, yayin daga bisani aka kai hari ta sama da jirage masu saukar ungulu.
A cewar jaridar, wani sojan ajiya ya rasa wayarsa ta hukuma a yayin hargitsin, wanda daga baya ta fada hannun wani dan ƙasa. Sojan ya bayyana cewa sojojin Isra'ila nan take suka toshe wannan na'urar daga nesa don hana bayyanin bayanai.
Rahoton ya ce ana daukar wannan lamari a matsayin "babban hadarin tsaro" a cikin sojojin Isra'ila, domin wannan na'urar tana dauke da bayanan soji masu muhimmanci.
Sojojin Isra'ila a cikin sanarwarsu sun ce ana ci gaba da binciken lamarin, kuma ana duba shi ta hanyoyin tsaro da suka dace.
A gefe guda, kafofin yada labaran Siriya sun fitar da hotuna da bidiyo da suka hada da kayan soji da kuma abubuwan da ake zargin suna da alaka da wayar da aka rasa.
A cewar rahoton, dakarun sojojin Isra'ila a yayin aikin da kuma lokacin da suka ja da baya, sun bar wasu kayan aiki da abinci a wurin.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kasancewa a kudancin Siriya, kuma ana samun rahotannin ayyuka lokaci-lokaci a yankuna daban-daban.
………………….
Your Comment