Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Isra'ila, a yau Lahadi, ta kai wani hari ta sama a kan wani ginin zama mai hawa biyar a unguwar Ghobeiri a unguwar kudancin Beirut, lamarin da ya kai ga shahadar mutane 3 da raunata 7, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen ya ruwaito.
Ta'addancin Isra'ila a kan unguwar kudancin Beirut ya zo ne a daidai lokacin da ake sa ran sanar da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Washington da Tehran don kawo ƙarshen yaƙi, abin da mamayar Isra'ila ke ƙin jinin hakan tana mai cewa yajejeniyar ba ta da kyau domin tana mai cutar da bukatun Isra'ila ne.
A ranar 7 ga Yuni, wannan watan, mamaya ta kai wani harin ta'addanci a kan wani ginin zama a unguwar Tahuital al-Ghadir a unguwar kudancin Beirut, lamarin da ya kai ga shahadar mutane biyu da raunata wasu. A matsayin martani ga wannan ta'addanci, Iran bayan 'yan sa'o'i, ta kai harin rokoki daga dama kan wuraren mamaya a cikin ƙasashen Falasdinu da aka mamaye.
Ta'addancin da aka kai wa unguwar kudancin Beirut, ya zo ne a cikin yanayin ci gaba da ta'addancin Isra'ila a kan Lebanon, duk da "tsagaita wutar" da aka sanar.
Ya kamata a tuna cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tana nanata cewa makomar yaƙi a Iran da Lebanon suna da alaƙa kut da kut, kuma ta tabbatar da cewa ko dai yaƙi ya tsaya a Iran da Lebanon tare, ko kuma kada ya tsaya a kasashen biyu. A cikin wata hira da ta gabata da Al-Mayadeen, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa duk wani ta'addanci a kan Beirut zai fuskanci martanin Iran, yana mai cewa: "Sakamakon wannan ta'addanci zai zama dawowar yaƙin, kuma wajibi ne mu tunkare shi".
……………………..
Your Comment