8 Yuni 2026 - 08:09
Source: ABNA24
Iran Ta Yi Amfani Da Sabon Jirgin Mara Matuki A Hare-Harenta Na Dare A Kan Isra'ila

Iran ta yi amfani da wani sabon jirgin mara matuki wanda ba a san cikakkun bayanansa ba, wanda ke aiki da injin Ingizawa, Injin Ingizawa wani inji ne da ke fitar da ruwa ko iska da sauri sosai don samar da ƙarfin ingiza abu bisa ga ka'idar motsin Newton ta uku.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Sayyid Muhammad Tahiri, jami'in da ke da alhakin harkokin soji a rukunin "Bayanan Yaƙi" na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim na Iran, ya bayyana cewa Iran a hare-harenta na dare a kan Isra’ila, ta yi amfani da wani sabon jirgin mara matuki wanda ba a san cikakkun bayanansa ba, wanda ke aiki da injin Ingizawa, a matsayin matakin da ya kira farkon bayyanar fasahar aikin irin waɗannan jiragen.

Ya bayyana cewa harin ya zo ne a matsayin ramuwar gayya ga wani harin da Isra'ila ta kaiwa yankin Dahiya ta kudancin Beirut, yana mai ganin cewa Tel Aviv ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta yi a baya.

Ya kara da cewa, aikin hadin gwiwa na Iran da makamai masu linzami da jirage mara mataki sun kai hari ga yankunan da aka mamaye, musamman sansanin sojan sama na Ramat David.

Tahiri ya yi nuni da cewa aikin yana ɗauke da saƙonni da yawa, mafi muhimmanci su ne tabbatar da shirye-shiryen Iran don kare ƙawayenta a yankin musamman Hizbullah, da kuma nuna jajircewarta wajen aiwatar da barazanar da gargaɗin da take yi wa abokan hamayyarta.

A bangaren soji, ya tabbatar da cewa harin ya yi amfani da makamai masu linzami na "Khaibar Shikan" da aka harba daga sansanonin yammacin Iran, yana mai bayyana cewa waɗannan makamai masu linzami, waɗanda aka bayyana su a shekarar 2022, suna da iyakar kimanin kilomita 1,400, kuma suna dauke da kawunan yaki mai yawan da ƙarfin motsawa da kuma kutsawa cikin tsarin kariyar makamai masu linzami. Ya kuma yi nuni da cewa lokacin shirye-shiryensu don harbawa bai wuce kusan mintuna 20 ba, wanda ke ba su damar aiki mai muhimmanci.

Tahiri ya kuma bayyana amfani da wani sabon nau'in jirage mara mataki na kunar bakin wake da ke da injin ingizawa, maimakon jirage mara mataki na gargajiya masu injin piston kamar "Shaheed 136". Ya yi nuni da cewa jirage masu injin ingizawa suna da sauri mafi girma wanda ke sa kama su ya fi wahala, duk da cewa suna cin man fetur da yawa, yana mai tunanin cewa jirgin da aka yi amfani da shi na iya zama mafi girma ga "Shaheed 136" saboda buƙatun zango da nauyi.

Ya yi ganin cewa makasudin shigar da wannan sabon jirgin a aikin na iya zama gwada aikinsa a yanayin yaƙi na gaske da kuma kimanta ƙarfinsa a fagen, a matsayin share fage don haɓaka da amfani da shi nan gaba a cikin kayan yaƙin sojojin Iran.

Ya ƙarasa da nuni da cewa Isra'ila ta bayyana aniyarta ta mayar da martani ga harin, yayin da Tehran ta yi gargadin cewa duk wani sabon martanin Isra'ila zai fuskanci martanin makamai masu linzami mafi fadi da tsanani, yana mai ganin cewa ƙa'idar fifikon juna tsakanin bangarorin tana ginuwa ne a kan ƙarfin soja fiye da hanyoyin diflomasiyya.

Wannna harin ya biyo bayan kalaman Mai ba da shawara kuma mataimakin babban jagoran Iran, Mohammad Mokhber, a cikin wani sako da ya buga a shafinsa, ya ce: "Makiya, ta hanyar jefa bama-bamai a Lebanon yayin da mai sasanci ke Iran, sun kunnawa teburin tattaunawar wuta a karo na uku,".

Mokhber ya kara da cewa wannan ci gaban "yana tabbatar da babbar murya game da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da suka yi a dukkan fagage," yana mai nuni da cewa Tehran tana ɗaukar wannan a matsayin wani mummunan tashin hankali a hanyar fuskantar juna.

Ya ci gaba da cewa: "Muna magana da masu karya alkawari da harshen ƙarfi, domin fagen gwagwarmaya jiki ɗaya ne mai cikakkiyen haɗin kai, kuma babu shakka za su ga sakamako mai tsada da raɗaɗi a fagen fama saboda wannan zalunci".

……………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha