Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Tare da himmar Babban Daraktan Ayyukan Al'adu da Bugawa na Majalisar Duniya ta Ahlul Bayt (A.S), an fassara kuma aka buga littafin "Imami Amirul Muminina Ali (A.S) a Mahangar Halifofi" da harshen Swahili.
Wannan littafi bayani ne da nazari game da martabar Imam Ali (A.S) da kuma tabbatar da fifikonsa a mahangar Halifofin Ahlus-Sunnah. Marubucin a cikin wannan littafi, ya yi kokari ta hanyar bincike a cikin hanyoyin ruwayoyi masu inganci na Ahlus-Sunnah, ya gabatar wa masu neman gaskiya wasu abubuwa daga cikin falalu da daraja da suka kebance Amirul Muminina (A.S) wadanda maƙiyansa na farko suka yarda da su kuma suka amince da su.
Muhimman Abubuwan Da Littafin Ya Kunsa Sune Kamar Haka:
1. Wasu hadisai daga Annabi (S.A.W) game da sifofin Ali (A.S) waɗanda Halifofin farko da wasu daga Halifofin Banu Umayya da Banu Abbas suka ruwaito;
2. Ikrarin da suka yi game da nau’oin fifiko da darajar da Imam (A.S) ya samu a fagage daban-daban kamar ilimi, takawa, halayya da siyasa, da kuma cewa shi ne wanda ya fi cancanta da riƙon matsayin magajin Annabi (S.A.W).
3. Tambayoyin ilimi da addini da neman shawarwarin siyasa da Halifofi suka yi wa Imam Ali (A.S) a lokacin da suka shiga cikin matsaloli.
4. Ikrarinsu ga gazawarsu a fannin ilimi da kuma tura masu tambaya zuwa ga Amirul Muminina (A.S).

Littafin Imam Ali (A.S) a mahangar Halifofi littafi ne da Mahdi Faqih Imani, wanda Kazim Abbas Lawaki Bebe ya fassara kuma an buga a nau’in takarda ta girman Waziri.
…………………..
Your Comment