2 Yuni 2026 - 09:57
Source: ABNA24
IRGC Sun Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Amurka Da Makami Mai Linzami Na Cruise

Sojojin Ruwa Iran sun  mayar da maratani ga harin da Amurka ta kai ga wani jirgin kasar in da suka kai hari kan jirgin ruwa mai suna "MSC Sariska" mai alaka da Amurka da Isra'ila da makami mai linzami na Cruise.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sojojin Ruwan Iran sun sanar da kai hari kan jirgin ruwa "MSC Sariska" mallakin abokan gaba na Amurka da Isra’ila.

Ofishin hulda da jama'a na Irgc ya bayyana a cikin wata sanarwa: "Sakamakon harin da sojojin Amurka masu ta'addanci makasa yara suka kai kan jirgin ruwan Iran "Lian Star" a yankin tekun Oman, Sojojin Ruwan Irgc, a ramuwar hakan sun kai hari kan jirgin ruwa 'MSC Sariska' mallakin Amurka da Isra’ila da makami mai linzami na Cruise".

Sojojin Ruwan sun kuma sanar da cewa duk wani hari daga bangaren sojojin Amurka makasa kashe yara a wannan yanki zai fuskanci da tsauraran martani.

………………………………………………

Your Comment

You are replying to: .
captcha