Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Hukumar Huldar Jama'a ta Dakarun Juyin Musulunci, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce: Dakarun Juyin Musulunci a Iran, da safiyar ranar Litinin, sun bayyana cewa mayakansu na sama sun kai hari kan sansanin sojan sama wanda daga gare shi ne aka kaiwa hasumiyar sadarwa a tsibirin Sirik da ke lardin Hormozgan hari.
Dakarun Juyin Musulunci a cikin sanarwar sun yi gargadin cewa idan aka sake yin irin wannan zalunci, to da martani zai bambanta.
Dakarun Juyin Musulunci sun jaddada cewa cikakken alhakin sakamakon harin yana kan gwamnatin Amurka mai zalunci wacce ke kashe yara.
A nata bangaren, rundunar Centcom ta Amurka ta bayyana cewa ta aiwatar da "hare-hare na tsaro" a kan wasu wuraren radar na Iran da wuraren bayar da umarnin jirage mara matuki a ranakun Asabar da Lahadi.
Ta kara da cewa "wadannan hare-hare sun zo ne a matsayin martani ga kakkabowar da Iran ta yi ga jirgin Amurka mara matuki nau'in MQ-1”.
………………………..
Your Comment