31 Mayu 2026 - 21:05
Source: ABNA24
Da'awar Isra'ila Na Sarrafa Ginin Ganuwar Al-Shuqif Farfaganda Ce Kawai Ba Nasarar Soji Ba

Sojojin Isra'ila da safiyar yau Litinin sun yi da'awar cewa sun kwace iko Ganuwar Al-Shuqif (Beaufort) a kudancin Lebanon. Amma manazarta da masu fafutukar kafofin watsa labarai sun ɗauki wannan matakin a matsayin farfaganda da ƙoƙarin Isra'ila don nuna nasara a kan abubuwan da suka faru a baya, sun jaddada cewa gwagwamayar Lebanon na ci gaba da addabar makiya tare da sabbin dabarun yaki da suka hada da ɓoyewa da hare-hare cikin sauri da jirage mara matuki da makamai masu linzami.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sojojin Isra'ila da safiyar yau Litinin sun sanar da cewa sun kwace iko da ganuwar "Al-Shuqif" Beaufort, wadda ke kan wani tudu mai tsayi sama da mita 700 da ke fuskantar kogin Litani, kwarin Al-Suluqi da garin Al-Matullah, bayan fafatawar da aka yi a filin daga tare da bude wuta mai tsanani ta ƙasa da sama.

A mayar da martani ga wannan matakin, Fouad Khreis, wani mai fafutukar kafofin watsa labarai, ya bayyana bidiyon da sojojin Isra'ila suka fitar a matsayin "hoton tallatawa" wanda ke nuna lokacin da aka mamaye ganuwar.

Ya jaddada cewa: Ganuwar wani "gine-ginen tarihi ne da yawon bude ido" ne, ba wata ganuwar mafakar mayaƙa ba.

Khreis ya ishara da cewa: Ana ganin sojoji a cikin wannan bidiyon ba tare da motocin yaƙi masu sulke ba, wanda ke nuna cewa sun kutsa cikin daga bayan katangar don yin wannan hoton talla da Netanyahu ke buƙata, sannan su ja da baya.

Tsarin Tsaro Na Gwagwarmaya Ya Canza

Yasin Ezzeddine, marubuci kuma manazarci, ya jaddada cewa: Kafofin watsa labarai na Isra'ila suna ƙara nuna girman wannan matakin na kwace ganuwar. In da ya bayyana cewa: A Yau salon tsaro ya canza gaba ɗaya; gwagwarmaya ba ta zama a cikin ganuwowi ko sansanonin soji, sai dai ta dogara da ramukan kasa da ɓoyewa don kai hare-hare da sauri da ban mamaki don addabar makiya, baya ga amfani da makamai masu linzami da jirage mara matuki masu ingancin yaƙi.

Ƙoƙarin Isra'ila Don Nuna Ta Yi Nasara A Kan Abubuwan Da Suka Faru A Baya

Tamer Qudih, ɗan jarida, shi ma ya dangana wannan ridin Isra'ila ga ƙoƙarin samun nasara a kan matsaloli da abubuwan da suka faru a baya ne, ba bisa ga bayanan abun da ke faruwa halin yanzu ba.

Ya yi nuni ga yaƙin 1982 inda sojojin Isra'ila na musamman suka yi asarar rayuka da dama kafin mamaye ganuwar, kuma Menachem Begin tare da Sharon suka ziyarci shahararriyar ganuwar don ɗaukar hoton nasara.

Qudih ya ishara cewa: Daga baya Ganuwar ta zama wata Ganuwar soji mai ƙarfi sosai da manufa dabara ga Gwagwarmayar Lebanon, waɗanda suka raunana ta da hare-haren makamai masu linzami da kwanton bauna har zuwa lokacin da suka ja da baya a shekara ta 2000.

Ya bayyana cewa: Yau wanda ke yaƙi a Lebanon yana amfani da dabarun yaƙi mai bazuwa ba tare da hare-hare ta sama ko tsarin tsaro ba, kuma a irin waɗannan yaƙe-yaƙe, ba za a iya hana ci gaban yanki na sojojin da ke kai hari ba, amma gwagwarmaya na da ikon addabar su har sai sun ja da baya.

A cikin tabbatar da ci gaba da yanayin addabar da Qudih ya yi magana akai, Khalil Nasrallah, ɗan jarida, ya yi nuni da cewa: 'Yan sa'o'i kaɗan bayan gabatar da mamaye Ganuwar Al-Shuqif a matsayin "nasara da take kare musamman garin Al-Matullah," an ji ƙararrawar haɗari a cikin wannan garin da sauran yankuna saboda saukar makamai masu linzami da aka harba daga Lebanon.

Babban Ƙalubalen Isra'ila: Ci Baya Ne Ba Ci Gaba Ba

Samer Haj Ali, ɗan jarida, shi ma ya jaddada cewa: Ka'idar filin tana nuna cewa mamaya zata iya isa kowane yanki a Lebanon, amma babban ƙalubalen yana cikin ikonsa na zama da jure wa farashin rayuwa. Ya yi nuni ga sauye-sauyen Al-Bayadah, Al-Labbounah, Zawtar da Yahmar, kuma ya jaddada cewa Al-Shuqif ma za ta fuskanci irin wannan yanayin ne.

………………………………….

Your Comment

You are replying to: .
captcha