Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito, Marco Rubio, ministan harkokin wajen Amurka, ranar Juma'a ya sanar da cewa: A yayin tattaunawar da ake ci gaba da yi da Iran, an samu wasu ci gaba na musamman.
Marco Rubio, ministan harkokin wajen Amurka, ya bayyana cewa: A matakin tattaunawa da shawarwari da Iran, muna ganin wasu ci gaba.
A wani bangare na jawabinsa game da abubuwan da ke faruwa a teku a yankin, ya yi gargadin cewa duk wata kawo tangarda a cikin safarar jiragen ruwa, in da ya yi iƙirarin: Na yi imani cewa babu wata ƙasa da za ta yarda cewa don wucewa ta mashigar Hormuz, dole ne ta biya haraji ko kudin wucewa. Irin waɗannan ayyuka gaba ɗaya ba su da karbuwa a duniya.
Ministan harkokin wajen Amurka ya yi iƙirarin: Ƙoƙarin tilasta kuma karɓar haraji daga safarr jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wani misali ne na karɓar haraji na zalunci, kuma babu wata ƙasa a duniya da za ta yarda da shi.
...............
Your Comment