Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jagoran Ansarullah: Maƙiyan Yemen suna neman mamaye wannan ƙasar ne. Ya kuma kara da cewa: "Al'ummar mu abin kauna ba za su amince da wani kwamitin hadin gwiwa na Amurka, Birtaniya, Isra'ila da Saudiyya ba".
Jagoran Ansarullah, ya taya 'yan ƙasar Yemen murnar ranar haɗin kan Yemen. Ya kara da cewa: "Masu iko na waje suna neman su mallaki cikakken iko a wannan ƙasa, su kwace 'yancinsu da 'yancin kai, su kuma yi amfani da matsayi da albarkatun ƙasar Yemen don muggan manufofinsu.
Sayyid bayyana cewa, abubuwa biyu masu muhimmanci da ke tabbatar da haɗin kan al'ummar Yemen su ne: ƙarfafa asalin haɗin kai wanda ya ginu akan imani, da kuma tabbatar da cewa wannan asali ya kasance mafarin haɗin kai, da tsarin 'yanci wanda shi ke kiyaye 'yancin kai.
Jagoran Ansarullah: Amurka Tana Son Ta Ceci Tattalin Arzikinta Da Kuɗaɗen Kasashen Larabawa Ne
Ya kara da cewa: Shugaban Amurkan yana alfahari kuma yana takama da cewa; domin ya dawo da wasu makudan kudade daga kasashen yankin tekun Farisa wadanda zai yi amfani da su wajen magance matsalolin tattalin arziki da rikice-rikicen da Amurka ke fuskanta".
"Lokacin da shugaban Amurka ya fuskanci manyan matsalolin tattalin arziki a Amurka, sai ya juya zuwa ga kasashen Larabawa, musamman kasashen tekun Farisa, domin samun tiriliyoyin daloli".
Ya kara da cewa: "Takunkumin tattalin arziki abu ne mai matukar muhimmanci wanda ya cancanci a kula da shi sosai a matakin wayar da kan jama'a".
.............................
Your Comment