Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Bayar da sammacin gwamnatin Amurka kan Raul Castro tsohon shugaban kasar Cuba mai shekaru 94 wani gagarumin juyi ne a cikin kusan shekaru 70 da Amurka ke fama da shi a wannan tsibiri.
Shugaban gwamnatin ta'addanci ta Amurka a cikin jawabinsa game da kasar Cuba, ba tare da yin ishara ga takunkumin zalunci na Washington ga al'ummar wannan kasar ba, ya yi iƙirarin cewa wannan kasa ce da ta sha kaye, ba su da wutar lantarki, ba su da kudi, hakika kusan ba su da wani abu, kuma za mu taimaka musu ne su ci gaba.
Saɓanin hakan Dubban masu zanga-zangar sun taru a gaban ofishin jakadancin Amurka a Havana don nuna adawa da yunkurin da gwamnatin ta'addancin Amurka ta yanke na gabatar da tuhume-tuhume ga Raul Castro, tsohon shugaban kasar Cuba.
................
Your Comment