Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wani jirgi mara matuki na kungiyar Hizbullah cike da bama-bamai ya afkawa wani wuri kusa da Karyat Shimona a arewacin yankunan da aka mamaye. Lamarin da tilasta wa jiragen sama masu saukar ungulu na Isra'ila sauka don kwashe mutanen da suka mutu da raunata. Rahoton tashar KAN game da tsoron sojojin Isra'ila wajen fuskantar jirage marasa matuƙa na Hizbullah. Cibiyar sadarwa ta Harshen Ibrananci "Kan" ta bayyana karara cewa sojojin Isra'ila sun shiga cikin mawuyacin hali saboda rashin iya magance matsalolin hare-haren jirage masu ɗauke da bama-bamai na Hizbullah. Ikirarin kafafen yada labarai na gwamnatin sahyoniyawan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun "mummunan hare-haren Hizbullah" a arewacin Falasdinu da kuma kai harin makamai masu linzami ba tare da kunna ƙararrawa ba, ya kara dagula tashin hankali da rashin tsaro a cikin sojoji. Dangane da haka, rahotannin cikin gida sun nuna cewa an samu asarar rayuka da suka wuce hankali a yankin Lebanon da aukuwar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a tsarin ma'aikatan sojojin. Babban hafsan sojin sahyoniyawan ya yi gargadi a tarurrukan sirri cewa tare da rage lokacin hidima da matsin lamba na yakin, sojojin ajiyar suna gab da rushewa kuma Isra'ila na rasa dubban sojojin kawo ɗauki na ko ta kwana.
Hizbullahi ta kai mummunan hari kan sojojin Isra'ila a arewacin yankunan da aka mamaye wanda harin yayi sanadiyar mutuwar sojojin da raunatar wasu.
Your Comment