8 Mayu 2026 - 16:52
Source: ABNA24
Sojojin Ruwan Iran Da IRGC Sun Gudanar Da Hare-Hare Biyo Bayan Harin Amurka

Binciken sirri ya nuna hare-haren sun haifar da gagarumar barna da lahani ga abokan gaba na Amurka, inda wasu jiragen ruwa guda uku na maƙiya da sauri suka tsere daga mashigar Hormuz. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar Sojan Ruwa ta IRGC ta rubuta a kan dandalin X: "Bayan karya tsagaita bude wuta da kar harin sojojin ta'addancin Amurka a kan wani jirgin ruwan Iran a kusa da tashar jiragen ruwa na Jask da kusancin jiragen ruwan Amurka zuwa mashigar Hormuz, an kai masu hari da wasu hare-hare mai tsanani mai inganci ta hanyar amfani da makamai masu linzami na ballistic iri-iri" masu lalata jiragen ruwa na yaki da jiragen sama marasa matuki inda su kai ta luguden wuta mai tsanani kan abokan gaba. 

Binciken leken asiri ya nuna haifar da gagarumar barna da lahani ga abokan gaba na Amurka, kuma wasu jiragen ruwa guda uku na maƙiya da sauri sun tsere daga mashigar Hormuz. A sanawarsa shi ma mai magana da yawun Sansanin Hazrat Khatam Al-anbia: Rundunar ƴan ta'addan da 'yan fashin Amurka sun karya yarjejeniyar tsagaita bude wutan inda suka kai hari kan wani jirgin ruwan Iran da ke tafiya daga gabar tekun Iran a yankin Jask zuwa mashigar Hormuz da kan wani jirgin ruwa da ke ƙoƙarin shiga mashigar Hormuz a gaban tashar jiragen ruwa na UAE na Fujairah. Har ila yau, sun kai hari kan yankunan farar hula tare da hadin gwiwar wasu kasashe a yankin da ke gabar tekun Bandar Khamir, Sirik da Qeshm. Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran su ma nan da nan kuma a wani mataki na mayar da martani sun kai hari kan jiragen ruwan sojin Amurka da ke gabashin mashigar Hormuz da kudancin tashar jiragen ruwa na Chabahar tare da yi musu barna sosai. Ya kamata masu aikata laifukan ta'addanci na Amurka da kasashen da ke tallafa ma ta su san cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kamar da tana cikin kololuwar iko kuma ba tare da ɗan ƙanƙanin shakku za ta mai da martani mai halakarwa ga duk wani keta iyaka da za ai mata.

Your Comment

You are replying to: .
captcha