Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wannan Marubucin Ba’amurke ya yi ikirari cewa an samu ɓaraka da ba a taba ganin irin ta ba tsakanin kwamandojin soji da fadar White House. Brendan Wychert, mai sharhi kan geopolitical ya ƙara da cewa: Ba a ba da cikakken rahoton wani ɓangaren labarin na abinda ya faru ba da ke cewa kwamandoji masu uniform, musamman a cikin sojojin ruwa, a zahiri sun yi tsayayya ga shugaban kasa. Shugaban ya so su yi kundibala su ketara mashigar, amma sojojin ruwa sun yi ƙoƙarin kaucewa hakan a ƙarƙashin kowane dalili suna masu cewa: A'a, yallabai, ba za mu iya hakan ba.
Kwamandojin sojojin ruwa na Amurka sun ki bin umarnin Trump kan aikin sojin da ya kira "aikin 'yanci"; suna masu cewa Iran fa ba wasa ta ke ba. Babbar matsalar Trump ita ce, hatta yayin da ya umarci kwamandojin sojojin ruwa na Amurka da su tsallaka mashigar Hormuz su karya kawanyar, babu wanda ya yi biyayya. Don haka idan ma ba a fara aikin "'yanci" da ma ta riga ta kare, kuma ba wai saboda tausayawar Trump ba ne saboda tsoronaa ne, domin da gaske yana son yiwuwar aikin, amma saboda babu wanda zai saurare shi...
Anan, Brandon Wychert masani kuma ƙwararre a harkar tsaro. Kwamandojin Sojojin Ruwa na Amurka suna adawa kaitsaye ga umarnin gwamnatin Trump. Amma ta yiwu Trump bazai gane ba, amma wadannan kwamandojin soji sun fahimta da kyau cewa Iran ba wasa ta ke ba kuma tafiyar tasu na iya kasancewa yana hannunsu, amma dawowa daga yaƙin ba ya hannunsu!
Your Comment