7 Mayu 2026 - 14:26
Source: ABNA24
Azzam Khalil Hayyah Yayin Shahada A Gazza

A martanin shahadar ɗansa, shugaban ƙungiyar Hamas yayi kira da cewa: Ya kamata Ƙasashen Duniya Su Tilasta Wa Tel Aviv Aiwatar Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tare da shahadar Azzam Hayyah, adadin 'ya'yan shahidai na Khalil al-Hayyah, shugaban ƙungiyar Hamas a yankin Gaza, ya kai huɗu. Azzam ya ji mummunan rauni a harin da sojojin mamaye na Isra'ila suka kai a Gaza jiya kuma daga ƙarshe ya rasu sakamakon tsananin raunin da ya samu, inda ya haɗu da sauran 'yan uwansa uku, Osama, Hamza, da Hammam.

Allah Ta'ala ya karbi shahadarsu ya kuma karfafi gwagwarmaya da jinanansu.

Khalil al-Hayyah, shugaban ofishin siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Gaza, a martanin shahadar ɗansa a wani hari ta sama da Sahayoniya suka kai masa, ya yi kira ga ƙasashen duniya da masu shiga tsakani da su tilasta wa Tel Aviv aiwatar da alkawuran tsagaita wuta da kuma dakatar da hare-haren wuce gona da iri a Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha