4 Mayu 2026 - 23:13
Source: ABNA24
Gobara Mai Girma A Cibiyoyin Man Tashar Jiragen Ruwa Ta Fujairah + Bidiyo

Hotunan tauraron ɗan adam sun nuna wata babbar gobara a wuraren mai na Tashar Jiragen Ruwa ta Fujairah. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tashar mai ta Fujairah ita ce hanya ɗaya tilo da za ta iya maye mamadin Mashigar Hormuz ga Hadaddiyar Daular Larabawa. Domin akwai bututun mai na ƙasa da ke ɗauke da ƙarfin ganga miliyan 1.5 na ɗanyen mai a kowace rana, wanda za a iya faɗaɗa shi zuwa ganga miliyan 1.8. 

An gina bututun ne musamman domin Hadaddiyar Daular Larabawa ta fitar da man fetur ba tare da ta ratsa ta Mashigar Hormuz ba. Harin ba wai kawai ya shafi abokan kawance ba ne, har ma ya shafi kayayyakin more rayuwa da ke ba da damar kwararar mai ba tare da ta ratsa ta Hormuz ba. 

Hanya guda daya tilo da za a bi don naye Mashigar Hormuz wadda ita ce bututun mai na Gabas-Yamma na Saudiyya zuwa Yanbu, wanda aka kai hari a watan Afrilu, wanda ya rage karfinsa da ganga 700,000 a kowace rana. 

Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi ikirarin cewa Iran ta kai hari kan cibiyoyin mai nata da ke tashar jiragen ruwa ta Fujairah a matsayin martani ga matakin Amurka da goyon bayan Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda Iran ta musanta kai hari kan Hadaddiyar Daular Larabawan. Bayan wannan harin an rufe makarantu a Hadaddiyar Daular Larabawa na tsawon kwanaki uku masu zuwa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha