Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Kafafen yada labaran Isra'ila waɗanda su kansu manyan masu goyon bayan yaƙi da Iran ne, a wannan karon an tilasta musu su fadar gaskiya. Gidan talabijin na Isra'ila Channel 12, ya ruwaito daga wasu manyan hafsoshin sojin wannan hukuma: "Amurkawa a zahiri ba su da ikon kare jiragen ruwan da ke wucewa ta mashigar Hormuz." Waɗannan majiyoyi sun bayyana dakatar da Aikin 'Yanci da Trump yayi a matsayin "hukunci mai ban mamaki a cikin yanayin rashin kwanciyar hankali da ke sake tabarbarewa," kuma sun jaddada cewa hanyar da Washington ta keɓe a madadin hakan wadda ke biye da gabar Oman, tana da haɗari matuƙa, ƙunci, da iyaka.
Kaskantar Da Wata Babbar Ƙasa Kamar Amurka A Aikace A Idon Duniya
Bayanan fage sun nuna cewa jiragen ruwan Amurka da ke yankin ba wai kawai sun kasa cika ikirarin rakiyar jiragen ruwan ba, har ma a aikace sun fuskanci martani kai tsaye da kakkausan nuna hannu daga sojojin Iran. Manazarta Amurka sun yarda cewa harba wasu makamai masu linzami da yawa zuwa jirgin ruwan yakin Amurka ya ragargaza tunanin fifikon sojan Amurka. Kanar Daniel Davis, tsohon sojan Amurka mai ritaya, ya fadi karara: "Mun aike da jiragen yaki guda biyu domin su rakiyi jiragen kasuwanci 2000. Wannan iƙirarin ba shi da ma'ana. Yayin da Iraniyawa ke cewa baza mu bayar da wani haraji ba, mu da kanmu babbar ƙasa ce, kuma iko a mashigar yana hannunmu".
Nasarar Da Ba A Taɓa Gani Ba Na Sojojin Ruwa Na IRGC Da Sojojin Iran
A tsakiyar wannan rikici, Sojojin Ruwa na Sepah (Pasdaran/IRGC) da Sojojin Iran, ta hanyar aiwatar da dabara mai cike da basira, sun kafa sabon tsari a mashigar Hormuz. Hotunan tauraron dan adam na Al Jazeera sun nuna yadda kwale-kwalen sojojin ruwan Iran suke a jera tare da sabbin iyakokin teku da Tehran ta sanar a ranar 4 ga Mayu, 2026. Sojojin Ruwa na Sepah, tare da sanar da ƙarin barazanar mahara ‘yan ta’addan Amurka, sun bayyana kafa sabbin ka'idoji don wucewa lafiya mai dorewa ga jiragen. A aikace, kusan jiragen ruwa 1500 suke makale a bayan mashigar Hormuz suna jiran izini daga Iran, kuma babu wani jirgin ruwa da ya amince da alkawuran Amurka a kan takarda.
Faɗuwar Dabaru Da Asara Mai Tsada Ga Kasashen Yamma Da Kawayensu
Rashin cin nasarar Aikin 'Yanci ya haifar da sakamako mai zurfi ga Amurka da kawayenta a yankin. Al-Mayadeen a wani sharhi ta rubuta: "Iran na iya girma a ƙarƙashin killacewa, amma Amurka da kawayenta ba za su iya ba." Tattalin arzikin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a matsayin ɗaya daga cikin manyan kawayen Washington, ya fadi sosai. Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Dubai ta fadi da kashi 4.7% kuma Abu Dhabi da kashi 3.3%, sashen otalotal na Dubai ya fuskanci raguwar kashi 80% na aiki, kuma ana siyar da gidaje da rangwamen kashi 12-15%.
Ƙarshen Yaƙi Da Jarumtakar Iran
Wannan rashin nasara a fagen fama ya tilasta Amurka da kawayenta su yarda da diflomasiyya cikin rauni. Rahotanni sun nuna cewa Tehran da Washington sun kusa sanya hannu kan yarjejeniya ta farko don kawo ƙarshen yaƙi da kwato kadarorin da aka killace na Iran. Joe Kent, wani tsohon jami'i a gwamnatin Trump, a martaninsa ga wannan rashin nasarar ya rubuta yana mai martani ga Trump: "Ka yi shelar nasara ka fice daga yaƙin. Ka dawo da sojojinmu gida." Robert Malley, babban mai tattaunawa a gwamnatin Obama, shi ma cikin izgili ga Trump ya rubuta: "Ina ja da baya saboda ina samun nasara sosai".
Aikin 'Yanci na Trump za’a rubuta shi a tarihi a matsayin alamar gazawar dabarun Amurka a gaban azama da ƙarfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Abin da Washington ta samu a aikace ba nasara cikin gaggawa ba ne, sai dai wulakanta da kaskanta tare da hauhawar farashin mai da kashi 60% a kasuwannin cikin gida da raunana amincin kawayenta, da kuma a ƙarshe amincewa da sabon tsarin teku wanda Sojojin Ruwa na IRGC da Sojojin Iran suke da babbar magana a cikinsa.
………………………………………………………….
Your Comment