1 Mayu 2026 - 18:22
Source: ABNA24
Jagora: Tekun Farisa Kyauta Ce Daga Allah Da Baƙi Suke Kwaɗayi

Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei ya bayyana cewa: "ɗaya daga cikin manyan ni’imomin da Allah Maɗaukaki Ya bai wa al’ummomin Musulmai a yankinmu – musamman ga mutanen ƙasarmu Iran mai daraja – ita ce kyautar “Tekun Farisa”. Ni’ima ce da ta wuce faɗin ruwa kawai, wadda ta zama wani ɓangare na asalinmu da al’adunmu, kuma ban da haɗa al’ummomi, ta zama hanyar tattalin arzikin duniya ta musamman wadda take bi ta Mashigar Hormuz zuwa Tekun Oman.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) nakaltowa daga Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, cikakkiyar fassarar rubutun saƙon Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, dangane da Ranar Ƙasa ta Tekun Farisa shi ne kamar haka:

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ɗaya daga cikin ni’imomin da ba a iya misaltawa na Allah Maɗaukaki ga al’ummomin Musulmai na yankinmu – musamman mutanen Iran ta Musulunci masu kirki – ita ce kyautar Tekun Farisa. Ni’ima ce da ta zarce tsurar ruwa kawai, wadda ta zame mana wani ɓangare na asali da al’adunmu; kuma ban da kasancewa hanyar da ta haɗa al’umma, ta kafa muhimmiyar hanyar tattalin arzikin duniya musamman a Mashigar Hormuz da kuma Tekun Oman. Wannan babban dukiya ta dabaru ta jawo kwaɗayin shaiɗanu da dama cikin ƙarnuka da suka gabata, da suka haɗa da mamayar Turawa da Amurkawa da dama, tsaro mara tabbas, asarar dukiya da barazanar da suka yi wa ƙasashen yankin, dukkansu wani yanki ne kawai na makircin masu girman kai a duniya kan mazauna yankin Tekun Farisa. Sabon misalin hakan shi ne wasan banza da babban shaiɗan (Amurka) ya yi kwanan nan.

Al’ummar Iran, wadda ke da kaso mafi yawa na bakin teku a Tekun Farisa, ita ce ta fi yin sadaukarwa wajen kare ’yancin Tekun Farisa daga mamayar baƙi; tun daga fitar da Fotugulawa da ƙwatar Mashigar Hormuz, wanda ya zama dalilin ayyana 10 ga Orbibesht (kalandar shamsi) a matsayin Ranar Ƙasa ta Tekun Farisa, har zuwa gwagwarmaya da mulkin mallakar Holland da kuma jarumtaka wajen yaƙi da mulkin Ingila, da sauransu. Amma Juyin Juya Halin Musulunci ne ya zama juyi mai muhimmanci da ya katse hannun masu girman kai daga yankin Tekun Farisa, kuma a yau – bayan watanni biyu na mafi girman mamaya da hari na azzaluman duniya a yankin – kuma da mummunan shan kashin Amurka, ana kan rubuta sabon babin Tekun Farisa da Mashigar Hormuz.

Al’ummomin yankin Tekun Farisa, waɗanda suka saba da shiru da karɓar ɗacin zalunci daga shugabanni masu rauni a gaban masu mamaya, sun shaida da idonsu a cikin kwanaki sittin da suka gabata jarumtar sojojin ruwa na rundunar sojan ruwa da na rundunar kare juyin juya hali (IRGC), tare da jarumtar mutane da matasa na kudancin Iran wajen ƙin mulkin baƙi.

Yau, da ikon Allah Maɗaukaki da albarkar jinin shahidanmu na yaƙin da aka tilasta mana na uku, musamman jagoran juyin juya hali mai girma wanda matsayinsa ya ɗaukaka, ba kawai a cikin ra’ayoyin jama’a na duniya da na yankin ba, har ma ga sarakuna da shugabannin ƙasashe ya tabbata cewa kasancewar Amurkawa a yankin Tekun Farisa – tare da sansanonin da suka kafa – ita ce babbar musabbabin rashin tsaro. Haka kuma sansanonin Amurka ba su da ƙarfin kare kansu, balle su kare mutanen da ke dogaro da su a yankin.

Da izinin Allah da ƙarfinSa, makomar yankin Tekun Farisa mai haske makoma ce ba tare da Amurka ba, wadda za ta kasance cikin hidimar ci gaba da jin daɗin al’ummarta. Mu da maƙwabtarmu a fadin Tekun Farisa da Tekun Oman muna da “ƙaddara iri ɗaya”, kuma baƙi da suka fito daga dubban kilomita suna kawo fitina a ciki, ba su da wurin zama sai dai a zurfin ruwansa. Kuma wannan sarkar nasara, wadda da yardar Allah Maɗaukaki ta tabbata bisa manufofi da dabarun “Iran mai ƙarfi”, ita ce shirin sabon tsarin wannan yankin da duniya gaba ɗaya.

A yau, tashin da ruhin al’ummar Iran ta yi ya zarce sadaukarwar miliyoyin masu yaƙi da Sahyoniyawa da Amurka mai shan jinin mutane. Miliyoyin mutanen Iran masu imani a cikin gida da wajen ƙasa – mutane miliyan casa’in – suna ɗaukar dukkannin albarkatun su na addini, kimiyya, masana’antu da fasahohin zamani (daga nano da bio zuwa nuclear da missile) a matsayin dukiyar ƙasa, kuma za su ci gaba da kiyaye su kamar yadda suke kare sararin ƙasarsu, samaniya da ruwayensu.

Iran Musulma, ta hanyar godiya a aikace ga Allah da damar shugabancin Mashigar Hormuz, za ta samar da tsaron yankin Tekun Farisa, kuma ta kawar da damar da abokan gaba ke amfani da shi. Ka'idoji da dokokin da sabon tsarin shugabancin Mashigar Hormuz za su samar da nutsuwa da ci gaba ga dukkanin al’ummomin yankin, kuma albarkatun tattalin arzikinsa za su faranta zukatan mutane – da izinin Allah, ko da kafirai ba su so ba.

Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei

10/Ordibehesht/1405 (30 Afrilu, 2026)

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha