26 Afirilu 2026 - 09:21
Source: ABNA24
Isra'ila Ba Ta Da Karfin Fuskantar Hizbullah

Wata kafar yada labarai ta Sahayoniya ta ba da rahoton gazawar sojojin wannan gwamnatin wajen fuskantar Hizbullah da tilasta ma ta yarda da tsagaita wuta.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafar yada labarai ta Sahayoniya "Israel Hayom" ta tona asirin gazawar sojojin gwamnatin Sahayoniya wajen fuskantar Hizbullah Lebanon yadda ya kamata, kuma ta bayyana cewa Tel Aviv, saboda rauni a fagen daga, ta zama dole ta yarda da tsagaita wuta.

Wannan jarida ta nakalto wani babban jami'in Sahayoniya cewa lamarin kawar da Hizbullah ta hanyar aikin soja, a halin da ake ciki, "ba abu ne dai iya faruwa ba ", kuma sojojin wannan gwamnati ba su da ikon gudanar da wani dogon yaki mai gajiyarwa.

A bisa wannan rahoto, ba a ba da wani umarni na aiki don kawar da Hizbullah ba, har ma jami'an soji sun yarda cewa babu wani makamin soja mai tasiri da zai iya cikakken dakatar da harben rokokin Hizbullah. A cewar waɗannan majiyoyi, ayyukan da ake yi a yanzu watakila kawai za su kai ga gajiyarwa mai iyaka ga Hizbullah, amma ba su da ikon gurgunta ta.

Wannan rahoto ya kuma yi nuni da tsananin gajiyawar aikin soja na sojojin gwamnatin Sahayoniya; yanayin da ya faru sakamakon yawaitar fagage da dogaro mai yawa ga dakarun ajiya, wanda hakan ya rage karfin yakin wannan gwamnati a fili.

Kamar yadda jaridar ta rubuta, aiwatar da wani aiki mai tsauri a kan Hizbullah yana buƙatar "ƙaruwar dakaru mai yawa" wanda a halin yanzu ba zai yiwu ba ga sojojin gwamnatin Sahayoniya. Don haka, zabin tsagaita wuta ba kawai shawara ce ta siyasa ba, har ma "larura ce ta aiki" don rage matsin lamba kan sojojin.

A ci gaba da wannan bincike, an ce gwamnatin Sahayoniya a zahiri ta ja da baya daga dabarun "nasara ta soja" kuma ta koma ga tafiyar da wani dogon yaki na gajiyarwa; dabarar da kawai ke iya takaita wa gwamnatin barazanar gwagwarmaya, amma ba kawar da ita ba.

A ƙarshe, wannan rahoto ya jaddada cewa Hizbullah ba ta sha kaye ba, kuma a lokaci guda farashin siyasa da na kasa da kasa na yakin ga gwamnatin Sahayoniya ya karu; ta yadda har a Amurka da Turai wannan matsin lamba ya ke karuwa don takaita tallafin da ake ba wa wannan gwamnati.

Your Comment

You are replying to: .
captcha