Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: shafin jaridar Axios ya ba da rahoton cewa shugaban Amurka Donald Trump, bayan jin karar harbi a bikin liyafar abincin dare na ƙungiyar 'yan jarida ta Fadar White House a birnin Washington, an fitar da shi daga bikin tare da tawagar tsaronsa.
A cewar rahotannin da aka wallafa, jami'an leken asirin Amurka da yawa a liyafar abincin daren ta ƙungiyar 'yan jarida ta Fadar White House sun ta yi ihun cewa: "An yi harbi!". A lokaci guda, gidan talabijin na CNN, ya nakalto wata majiya yana cewa rahotannin farko sun nuna cewa an kama mai harbin a otal din Hilton - inda taron yake gudana.
Wata majiya ta shaida wa gidan talabijin cewa Trump yana cikin koshin lafiya. A cewar wani jami'in gwamnati, mambobin majalisar ministocin kuma ba su samu wani rauni ba. Fox News kuma ta nakalto wata majiya tana cewa an ji karar harbi a otal din Hilton na birnin Washington, inda Trump ya halarci bikin liyafar cin abincin dare na 'yan jarida na Fadar White House. Kafofin watsa labarai na Amurka sun kuma bayyana cewa Trump da mataimakinsa sun fice daga wurin bikin liyafar cin abincin 'yan jarida na Fadar White House bayan jin wata babbar kara a cikin zauren.
A halin da ake ciki, wani dan jaridar jaridar Washington Post ya ce wata mummunar kara, wadda ake kyautata zaton ta fito daga harbin bindiga, ta katse taron liyafar cin abincin na 'yan jarida na Fadar White House.
Ya kara da cewa jami'an leken asirin Amurka sun fara aiwatar da tsarin fitar da wasu ministocin, ciki har da Marco Rubio, sakataren harkokin wajen kasar. Wani dan jaridan gidan talabijin na BBC a birnin Washington ya bayar da rahoto daga taron cewa mahalarta liyafar sun fake a karkashin tebura yayin da hargitsin tsoro da rudani ke faruwa a lokacin wannan lamarin.
Your Comment