Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mediterranean a cikin wani rahoto ta bayyana cewa wawashe da ƙwace dukiyoyin fararen hula ya zama wata siyasa mai aiki da haɓaka cikin ayyukan sojojin gwamnatin Sahayoniya, kuma ta bazu daga zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan har zuwa kudancin Lebanon.
Wannan hukuma ta jaddada cewa ƙungiyoyinta na fage sun rubuta rahotanni da yawa na satar dukiyoyin 'yan ƙasa a kudancin Lebanon, wanda ke nuna wani shiryayyen tsari bayyananne da shiri na wawashe dukiyar al’umma. An ga Sojojin Sahayoniya a fili yayin da suna ƙwace kekuna, kayan aiki, kayan gida da abubuwa masu daraja, suna masu kai su cikin motocin soji. Haka kuma shaidar 'yan ƙasar Lebanon ta nuna cewa sojojin mamaya sun yi ta satar zinare, kayan fasaha da kayan kiɗa daga cikin gidajen al’umma.
Wannan hukumar kare hakkin bil adama ta bayyana cewa abubuwan da aka rubuta a Lebanon ci gaba ne da wannan shiryayyen tsari mai fadi wanda aka riga aka aiwatar a zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan.
A cewar wannan hukuma, wawashe dukiyoyi na sirri haramun ne bisa dokokin ƙasa da ƙasa, kuma bisa ga yarjejeniyar Geneva da kundin Rome, laifi ne na yaki bayyananne.
Wannan hukuma ta bukaci a fara gaggauta bincike mai zaman kansa na ƙasa da ƙasa don tattara shaidu da tantance alhakin laifuka na mutanan da suka aikata wadannan laifuka a wannan fanni.
Wannan hukumar kare hakkin bil adama ta kuma bukaci gwamnatin Lebanon da ta shiga kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa don hana masu aikata laifuka samun kariya.
A ƙarshe, wannan hukuma ta bukaci al'ummar duniya da ta mayar da martani ga waɗannan ayyuka ta hanyar sanya takunkumi mai fadi a kan gwamnatin Sahayoniya, dakatar aikewa da makamai da goyon bayan siyasa.
Ya kamata a lura cewa jaridar Sahayoniya Haaretz a baya ta ba da labarin satar dukiyoyi da kadarorin mutanen kudancin Lebanon da sojojin gwamnatin Isra'ila suka yi.
Gidan talabijin na Al Jazeera na Qatar, a nakaltowarsa daga jaridar Sahayoniya Haaretz, ya kara da cewa an samu shaidu daga sojojin gwamnatin Isra'ila game da yadda sojoji ke satar ɗimbin dukiyoyin fararen hula daga gidaje da shaguna a kudancin Lebanon.
Wannan jaridar Sahayoniya ta ce satar babura, talabijin, kayan fasaha da kafet daga gidaje a kudancin Lebanon da sojojin Isra'ila ke yi ya zama ruwan dare kuma na yau da kullun.
Haaretz ta kara da cewa manyan kwamandojin soji da na ƙasa, a fagen yaƙi, suna da cikakken masaniya game da hanyoyin wawashewa da satar da sojojin Isra'ila ke yi a kudancin Lebanon, amma ba su ɗauki wani mataki na hana su ba.
Wannan jaridar Sahayoniya ta yi nuni da cewa sojojin gwamnatin Isra'ila a martaninsu sun ce za su dauki matakan ladabtarwa da na laifuka idan ya cancanta, kuma rundunar 'yan sandan soji za ta gudanar da bincike a mashigar kan iyaka ta arewa yayin da suke ja da baya daga yaƙin.
Your Comment