Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gwagwarmaya islama ta Lebanon ta gudanar da ayyuka hudu a matsayin martani ga keta yarjejeniyar da gwamnatin Sahayoniya ta yi. Sakamakon wannan aiki, daya daga cikin dakunan gudanar da buɗe wuta na abokan gaba ya kama wuta. 1- Da karfe 11:00, a matsayin martani ga ci gaba da mamaye kauyukan kudancin Lebanon bisa anfani da manyan bindigu Mujahideen sun kai hari kan sabon ɗakin da sojojin abokan gaban Isra'ila ke amfani da shi wajen kai hare-hare a birnin Al-Bayad bisa amfani da jiragen marasa matuka inda wuta ta kama a ɗaya daga cikin ɗakunan umarni buɗe wuta.
2- Da karfe 18:00 mayakan Hizbullah sun kai harin kan mota a birnin Al-Tiri da jirage marasa matuƙa n da jiragen sama marasa matuki a birnin Al-Qantara.
3- Da karfe 18:00, a martani ga kai wa birnin Yahmar al-Shaqif harin jirgin sama, Mujahidan gwagwarmayar Musulunci sun kai hari kan taron sojojin Isra'ila a birnin Qantra da jirage maras matuki.
4- Da karfe 18:00, a matsayin martani ga keta iyakar sararin samaniyar kasar Lebanon, mujahidai na gwagwarmayar Musulunci sun harbo jiragen leken asiri 4 da ke da alaka da sojojin makiya Isra'ila a birnin Al-Mansouri. Gwagwarmayar Musulunci ta dukufa wajen kare kasarta da jama'arta, musamman ta hanyar ketare iyaka da laifukan da Isra'ila ke aikatawa, kuma wannan shi ne aiki mafi karancin da zasu iya yi wajen hana ci gaban manufofin makiya masu hadari a kan Lebanon a matsayin kasa, al'ummar gwagwarmaya. Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, a matsayin mayar da martani kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Sahayoniya ta yi, ta kai hari kan wani gungun sojojin Isra'ila a kauyen Tayyiba da ke kudancin Lebanon da wani jirgin sama mara matuki. Sannan Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Lebanon ta sanar a cikin wasu bayanai daban-daban cewa ta gudanar da sabbin ayyuka da dama kan wuraren sojojin gwamnatin sahyoniyawan a kan iyakokin kudancin Lebanon. Wadannan ayyuka sun hada da kai hari kan tarukan sojin Isra'ila da kuma harbo jirgin leken asirin sojojin Isra'ila.
Your Comment