23 Afirilu 2026 - 16:37
Source: ABNA24
An Gano Gawar Shahida Amai Ƴar Jaridar Lebanon 

Yar jaridar Lebanon Ta Yi shahada a wani mummunan hari da Isra'ila ta kai mata. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: 'Yar jarida Amal Khalil ta yi shahada bayan mummunan harin da Isra'ila ta kai wa garin Al-Tayri da ke kudancin Lebanon. Amal Khalil, 'yar jaridar jaridar Al-Akhbar ta Lebanon ce tare da wata 'yar jarida mai suna Zainab Faraj, gwamnatin Isra'ila ta kai hari a garin Al-Tayri jiya da yamma. 

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Lebanon ta sami damar gano Zainab Faraj da ta ji rauni sannan ta kai ta asibiti. Majiyoyin Lebanon sun ce sojojin Isra'ila sun bude wuta kan motocin Red Cross kuma sun hana yunkurin fitar da Amal Khalil. 

Daga bisani an gano gawar 'yar jaridar Lebanon Amal Khalil a karkashin baraguzan ginin bayan sa'o'i da dama na bincike. Ta yi shahada a harin Isra'ila, bayan da sojojin Isra'ila suka bude wuta kan motocin daukar marasa lafiya da ke kokarin isa gare ta, lamarin da ya jinkirta aikin ceto. Ita ce 'yar jarida ta hudu da Isra'ila ta kashe a lokacin aiki tun daga ranar 2 ga Maris.

Your Comment

You are replying to: .
captcha