21 Afirilu 2026 - 09:49
Source: ABNA24
Yan Uwa Musulmi A Najeriya Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Iran Da Falasdinu + Hotuna

An rufe Mu'utamar Na Kasa da Kasa karo na 5 a garin Bauchi. Taron wanda Dandalin Dalibai da Malamai tare da haɗin guiwar Dandalin ƴan uwa Mata na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) suka shirya, mai taken 'Halin da ake ciki: ina mafita?"

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Taron wanda aka soma tun daga ranar Alhamis 16 ga watan Afrilun 2026, har ya zuwa yau Lahadi 19 ga Afrilun 2026, ya samu halartar ɗimbim ƴan uwa daga sassa daban-daban na ciki da wajen ƙasar nan.

A yayin taron a tsawon waɗannan kwanaki, manyan malamai da masana na ciki da wajen Najeriya sun gabatar da jawabai tare da tattaunawa kan halin da ake ciki tare da kawo mafita. Kazalika an tattauna batutuwa akan tattalin arziƙin ƙasar Amurka da siyasar ta da yadda suke aiwatar da hare-haren haɗin guiwa da Isra'ila na tsokana kan jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin taron, an gabatar da taron ƴan jaridu domin isar da saƙon manufofin Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) zuwa ga sauran al'umma.

A ƙarshe, Jagora Shaikh Zakzaky (H) ya rufe taron da jawabi wanda aka haska wa mahalarta ta hanyar majigi daga gidansa dake Abuja. Sannan aka gabatar da gangamin nuna goyon bayan ga al'ummar Falasɗinu wanda haramtacciyar ƙasar Isra'ila ke ci gaba da kashewa a kullum, tare da nuna goyon baya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da take fuskantar manyan masu girman kai na duniya.

An kammala taron lafiya kamar yadda aka fara shi lafiya.

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

01/DhulQaada/1447

19/04/2026

Your Comment

You are replying to: .
captcha