Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da zanga-zangar ne don mayar da martani ga kiran da kungiyar National Action Group domin Falasdinu, kuma mahalarta sun rera taken neman a kawo karshen daidaita dangantaka da "Isra'ila" da kuma yanke hulda da wannan gwamnatin gaba daya.
Masu zanga-zangar sun tashi daga dandalin Babul-Ahad da ke tsakiyar Rabat, kuma bayan sun yi tafiya ta hanyoyi daban-daban a fadin birnin, sun isa gaban majalisar dokoki da tashar jirgin kasa ta Rabatul-Madina. Lauyoyi, 'yan siyasa, kungiyoyin kwadago da dalibai masu fafutuka, tare da 'yan kasa daga yankuna daban-daban na kasar, sun halarci gangamin.
Your Comment