22 Afirilu 2026 - 20:49
Source: ABNA24
Ansarullah: Bai Kamata Mu Bar Amurka Da Isra'ila Su Sami Iko A Kan Al'ummarmu Ba

Sayyid Abdul Malik Badrudl-Din AlHouthi ya yi bitar sabbin abubuwan da suka faru a yankin a cikin jawabinsa kuma ya ce hare-haren da sahayoniya da Amurka suka kai wa al'ummar Musulunci sun shiga wani mataki mai hatsari. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban Ansarullah Yamen: Bai kamata mu bar Amurka da Isra'ila su sami iko a kan al'ummarmu ba kuma dole ne mu tsaya tsayin da ka wajen fuskantar masu girman kai da mamayar makiya. Shugaban ya kara da cewa: Batutuwa kamar canza fuskar Gabas ta Tsakiya yaudara ce kuma ƙarya ce kawai. Makiya suna ƙoƙarin yaudarar mutane ta hanyar kanun labarai da kokarin fahimtar da al'umma kan abinda suke yi akansu. Idan al'umma ta yi biyayya ga tsarin ƙa'idodi, dabi'u, da umarnin Musulunci, za ta yi nasara ta yunkura. Tun daga farkon yunkurin makiya sun yi ƙoƙarin ganin yanayin sallamawa da yin shiru tare da rufe bakinsu, da hana duk wani motsi da ya saɓa wa shirinsu. 

Makiya suna ƙoƙarin kai hakikanin yanayin Larabawa da Musulunci zuwa ga sukar laifukan Isra'ila kawai. A wasu ƙasashen tekun Farisa har ma ya zama suna kama mutane don sun yaɗa tweetar goyon bayan Falasdinu.

Bisa umarnin hukumomin tsaro, an haramta duk wani nuna goyon baya ga Hizbullah da al'ummar Lebanon kan harin Isra'ila. Yayin da aka haramta yin addu'a kan maƙiya da kuma yin Allah wadai da laifukan Yahudawa, bayyana aminci ga Isra'ila da kuma ba da hujjar dalilan laifukanta halattacce ne kuma har ma ana ƙarfafa su. Maƙiya suna son sanya shiru a duniyar Musulunci da kuma danne duk wani martani game da zaluncin Amurka da Isra'ila. Komai yawan laifukan da Yahudawan Sahyoniyawa ke aikatawa, daga Gaza zuwa wasu sassan Al'umma, har ma da sukar baki a wasu ƙasashen tekun Farisa ba a yarda da su ba. Danne muryoyin goyon bayan Falasdinu a wasu ƙasashen tekun Farisa ya fi muni fiye da na Amurka, Birtaniya da Turai.

Your Comment

You are replying to: .
captcha