23 Maris 2026 - 21:24
Source: ABNA24
Cikakkun Bayanai Kan Harba Gungun Makamai Karo 77 Wa’adi Sadiq + Bidiyo

Dakarun Iran sun kara kai gungun hari karo na 77 da ramzin:  "Ya Haidar Karar" sadaukarwa ga masu ba da labari na gwagwarmaya: "Shahidi Ali Mohammad Naeini", "Shahid Abu Ubaydah" da "Shahidi Mohammad Afif" a kan wuraren abokan gaba na sahyoniyawa a arewa da tsakiya da kudancin yankunan da aka mamaye da manyan makamai masu nauyi na Khaibar Shikan da jiragen yaki marasa matuki

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Dakarun Iran sun kara kai gungun hari karo na 77 akan kan wuraren abokan gaba na sahyoniyawa a arewa da tsakiya da kudancin yankunan da aka mamaye da sansanonin sojojin ta’addanci na Amurka da suka hada da sansanin Ali-Salim da Al-Kharj da Al-Zafrah, an kai hari ne da manyan makamai masu nauyi na Zulfiqar da Khaibar Shikan da jiragen yaki marasa matuki masu lalata komai suka hara’ an gudanar da kai harin da cikakkiyar nasara da yardar Allah.

Yanayin mu’amalar mayaudarin shugaban Amurka ba zai sa mu yi watsi da fagen fama ba za mu ci gaba da yaƙi da maƙiya, saboda aikin da Trump ya yi ya zama borin kunya don yaudarar da tunanin al’umma. Jajircewa da tsayin daka da gwagwarmaya na al’ummar Iran madaukakiya ya haifar da firgita da shakku a cikin tsare-tsare da al'amuran abokan gaba masu zalunci, kuma wannan tsayin daka mai daraja ya ci gaba a matsayin mabuɗin nasara. Za a ci gaba sanya makiya ja da baya tare da kasancewar al’umma a kan titi da kuma ci gaba da kai farmaki a fegen daga Insha Allahu har sai an samu nasara ta karshe.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha