Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A yau ne Jamus da Biritaniya suka yi watsi da bukatar Trump a hukumance inda suka ce ba su da wani shiri na tura jirgin ruwa zuwa mashigir Hormuz.
Bayan Kasashen da Trump ya nemi su taimaka masa wajen sake bude mashigir Hormuz sun noƙe hakan ke nuna rugujewar mulkin Amurka da kuma tsarin kawance da tasirinsa.
Gwamnatin Jamus ta sanar da cewa ba za ta shiga cikin yakin da ake yi da Iran ba kuma ba za ta yi wani kokarin soji na bude mashigin Hormuz ɗin ba.
Girka ta kuma yi watsi da bukatar Trump na neman taimako tare da sanar da cewa ba zata shiga cikin wani aikin soja a mashigin Hormuz ba.
Masana a Amurka sun ce: Babu wani tanadin doka a cikin yarjejeniyar NATO da ke bawa wata ƙasa tilastawa wata ƙasa shiga yakin zalunci da wata memba ta fara ba.
Your Comment