11 Maris 2026 - 23:48
Source: ABNA24
Iran Tana Ci Gaba Da Samun Nasara Wajen Harbo Jiragen Yaƙin Amurka Da Isra'ila

An gano jirage nau'in UAV guda 104 tare da Kakkaɓo su a cikin sa'o'i 24 da suka gabata kaso 95 na jiragen yaƙi marasa matuƙa masu kai hari ne aka kakkaɓo. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Makamai masu ɗauke da ton 2 nau'in Khorramshahr ya afkawa hedkwatar rundunar sojojin ruwa ta biyar na abokan gaba na Amurka bayan an harba shi daga Iran. 

Sannan an kai hari da Makamai masu linzami a yankin Kurdistan na Iraki kan sansanin Al-Harir na Amurka kusa da Erbil tare da aukar da barna sosai. 

Iran ta harbo jiragen yaƙi marasa matuka 11 da jirgi nau'in UMQs9 na Amurka, 

Majiyoyin labara sun ambata daga jami'an Amurka guda biyu cewa: tun farkon yakin, Iran ta harbo UMQs 9 11 masu daraja da ci gaba. 

A cewar jami'an Amurka, an kiyasta jimillar tsadar kudin da aka kashewa jiragen saman da sama da dala miliyan 330. 

Ana amfani da waɗannan jirage marasa matuki don leƙen asiri, sa ido da ayyukan bincike, da kuma ingantattun ayyuka. Rundunar sojin Iran ta sanar a cikin sanarwar 22 cewa, kawo yanzu sojoji da tsarin tsaro na IRGC sun harbo jiragen sama marasa matuka nau'ika da dama na Amurka da sahyoniya 102.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha