19 Janairu 2026 - 17:16
Source: ABNA24
Iran: Mun Himmatu Wajen Gudanar Da Ayyukanmu Don Magance Matsalolin Al'umma

Shugabanin Iko A Iran; Shugaba Massoud Pezeshkian, Kakakin Majalisa Mohammad Baqer Qalibaf, da Hujjatul-Islam Wal Musulmin Ejei, shugaban sashin shari'a, a cikin wani sakon hadin gwiwa yayin da suke godiya da jinjinawa ga al'ummar Iran masu daraja da fahimta da sanin lokaci suka iya karya tarkon makiya cikin mafi sarkakiyar makircin makiya masu adawa da hadin kan Iran mai karfi da ƴanci, sun ce: Mun himmatu wajen yin aiki ba dare ba rana don magance matsalolin rayuwa da tattalin arziki da tabbatar da tsaron jama'a, kuma zamu taba yin sakaci wajen gudanar da ayyukanmu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban sashin shari'a, Mohseni Ejei ya ce: Za a zartar da hukuncin shari'a ga masu tunzurawa a aikata laifuka da wadanda suka aikata ayyukan ta'addancin da hannusu a cikin lamarin da suka faru a baya-bayan nan. 

Yanke hukuncin Shari'ar zai gudana kan lokaci da hukunta masu aikata laifuka da ke da hannu a abubuwan da suka faru na baya-bayan nan, musamman manyan ƴan ta'addan da suka cancanci hukunci mai tasiri. Masu aikata laifuka, masu tayar da hankali tabbas doka za ta yi shari'a da hukunta su, tare da cikakken daidaito cikin sauri da adalci.

Ejei: Ba zamu taɓa ɗan jinkiri ba wajen gudanar da hukumci akan manyan masu tarzoma ba. 

Zartar da hukuncin ga masu tarzoma shine bukatar al'umma, kuma dole ne mu lura cewa aiwatar da hakan akan lokaci ba tare da bata lokaci ba yana daya daga cikin abubuwan da ke hana aiwatar da ayyukan tarzoma. 

Kamar yadda Jagoran juyin juya hali na juyin juya hali ya ke cewa: Ba zamu mu bar bibiyar masu aikata laifuka na baya-bayan nan a kotunan cikin gida da na kasa da kasa ba. Bisa la'akari da lalata dukiyoyin jama'a da na daidaikun mutane a cikin tarzomar, masu aikata laifuka da jagororinsu da waɗanda suka sanya su aikata wadannan abubuwan dole ne baya ga hukunta su su kuma biya diyyar wadannan asarorin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha