19 Janairu 2026 - 21:23
Source: ABNA24
Jiragen Yaƙin Isra'ila Sun Kai Hare-Hare Kudancin Lebanon

Isra'ila ta kai munanan sabbin hare-hare a yankunan kudancin Lebanon

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin Isra'ila sun kuma yi ikirarin cewa sun kai hari kan wasu wurare da ke da alaƙa da Hizbullah a Lebanon a kudancin kasar.

A cewar majiyoyin Isra'ila, hare-haren sun kai hari kan kwarin Barghez, kusa da sansanin Mays Ansar da Mahmoudiyah a kudancin Lebanon.

Sannan Shafin Al-Mayadeen ya ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun kai hari kan yankunan tsaunuka na yankunan Al-Tuffah da Al-Rayhan, da kuma yankunan Mahmoudiyah, Barghez da Ansar a kudancin Lebanon.

Sojojin Isra'ila suna masu ikirarin a cikin wata sanarwa cewa sun kai hari kan wuraren kungiyar Hizbullah ta Lebanon a wannan hare-haren.

Gwamnatin Isra'ila ta ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Lebanon tun daga karshen watan Nuwamba na 2024.

Your Comment

You are replying to: .
captcha