17 Janairu 2026 - 14:15
Source: ABNA24
Isra'ila: Kisan Kai Da Kai Na Sojoji Yana Ƙaruwa Da Kashi 40%.

Sojoji Isra'ila na ci gaba da kashe kansu da kansu saboda kuncin Rayuwa da tsananin tsoro da razani dake kara addabarsu saboda kisan kiyashin da suke yi a Falasɗinu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar yakin gwamnatin Isra'ila a cikin wani rahoto ta nuna karuwar kashi 40% na shari'o'in kisan kunar bakin wake sakamakon tsananta tabin hankali a tsakanin sojojin gwamnatin. 

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito a ranar Asabar cewa fiye da shekaru biyu Sojojin na yaki a Gaza da Lebanon a yanzu sakamakon waɗannan yakokin sun haifar da tabarbarewar tabin hankali a tsakanin sojoji, musamman ma sojojin da kota kwanta. 

A cewar jaridar, ma'aikatar yaki ta Isra'ila ta sanar da karuwar kashe kansu da kashi 40%, kuma idan ba a magance tsarin lafiyar jami'an sojin gwamnatin ba, za mu jira lamarin ya bunkasa a cikin shekaru masu zuwa. 

A cewar majiyoyin Isra'ila, tun farkon yakin Gaza, an ba da rahoton kasan kai 74 da yunkurin kisan kai wanda bai nasara ba da adadinsu ya kai 279.

Rahotanni sun ce kashi 60% na sojojin da suka jikkata suma suna fama da tabin hankali a lokaci guda. Damuwa, tsananin firgici, mafarki mai ban tsoro, da damuwa rashin barci sune manyan lamuran da iyalai suka ruwaito da suka dawo daga yakin. Dangane da haka, kungiyar Macabi Psychotherapy ta kuma ba da rahoton cewa kashi 39% na sojojin Isra'ila da suka yi yaƙi a Gaza ko wasu yankuna, bayan sun dawo, sun bukaci samar da shawarwari ko sabis na tabin hankalin ɗan adam.

Your Comment

You are replying to: .
captcha