Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Za’ai jana’izar gawar marigayi Ayatullah Sayyid Hadi Sistani, dan uwan Ayatullah Uzma Sayyid Ali Sistani, daya daga cikin manyan marjao’in 'yan shi'a duniya, a Qom.
Za a gudanar da wannan taron ne a yau (Lahadi, 18 ga Janairu) da karfe 3:00 na yamma daga Masallacin Imam Hassan Askari (AS) da ke Qom zuwa Haramin Sayyidah Ma’asumah (AS).
Haka kuma za a gudanar da zaman makoki marigayi Ayatullah Sayyid Hadi Sistani a wannan rana a masallacin Sayyidah Khadijah (As) dake a Maidan Moallem Qom, bayan Sallar Magrib da Isha.
Yana da kyau a ambata cewa Ayatullah Sayyid Hadi Sistani ya kasance daya daga cikin fitattun malaman makarantar hauza da suka shafe rayuwarsa suna inganta ilimin Musulunci da hidimar makarantar Ahlul Baiti (AS), wanda bayan wani lokaci na rashin lafiya aka kwantar da shi a asibiti a daya daga cikin Asibitocin da ke Tehran wanda ya koma ga ubangjinsa.
Your Comment