19 Janairu 2026 - 21:59
Source: ABNA24
Iraqi: Ta Aike Da Rundunar Hashdush Sha'abi Zuwa Iyakokinta Da Siriya

Bayan da 'Yan ISIS gudu daga gidajen yarin Siriya Iraqi ta tura dakarun Hashdush Sha'abi zuwa kan iyakokinta da Siriya domin hana shigowarsu

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Bagadaza, bayan wata yarjejeniya da aka cimma jiya da daddare tsakanin wakilan Damascus da Kurdawan Siriya da aka sani da Sojojin Demokradiyya na Siriya (SDF) da kuma tserewar dubban fursunonin ISIS daga cibiyoyin tsare-tsare na SDF, Rundunar Sojojin Hashdush Sha'abi Iraki ta dauki alhakin tabbatar da tsaron wannan yanki ta hanyar tura sojojinta zuwa kan iyakar da ke tsakanin Siriya da Iraki.

Tserewar gomman yan ta'addan ISIS daga cibiyoyin tsaresu na SDF ya sa gwamnatin Iraki ta dauki matakan kariya tun daga safiyar yau don hana yiwuwar shigar wadannan 'yan ta'adda cikin kasar.

Dangane da wannan batu, rundunar Hashdush Sha'abi a lardin Nainawa ta tura rundunoninta na yaki zuwa yankunan kan iyaka na wannan lardin da gabashin Siriya don hana duk wani yunkurin da 'yan ISIS ke yi na shiga yankin Iraki ko aiwatar da ayyukan ta'addanci.

Bugu da kari, kuma wasu daga cikin sojojin Hashdush Sha'abi suna zaune a hasumiyai a yankunan kan iyaka na wannan lardin. 

An kuma tura wasu daga cikin dakarun gaggawa na rundunar sojojin a yankin kan iyaka tsakanin Iraki da Siriya.

Iraƙi ta jaddada tabbatar da tsaron iyakokin da ke tsakaninta da Siriya da kuma ƙarfafa kasancewar rundunar sojojin Hashdush Sha'abi a kan iyaka.

Saad Maan, kwamandan hedikwatar rundunar sojojin haɗin gwiwa ta Iraki, ya jaddada a yau (Litinin) cewa tsaron iyakokin Iraki sun kasance cikin cikakken tsaro. 

Rundunar sojojin Hashdush Sha'abi ta kuma ƙarfafa kasancewarta a yankin kan iyaka da Siriya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha