Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wakiliyar Majalisar Tsaron MDD A Sudan tace Waɗannan laifukan sun faru ne musamman a ƙarshen Oktoba, lokacin da RSF ta mamaye birnin.
Ta ƙara da cewa: Bidiyon da muka yi nazari a kansu sun nuna cewa laifukan sun faru ne a sassa daban-daban na Darfur: kashe-kashe, daure mutanen da ba Larabawa ba, da kuma lalata gonaki da kayayyakin more rayuwa da ƙungiyar ta yi.
Shaidu daga majiyoyi daban-daban sun tabbatar da cewa ƙungiyar ce ke da alhakin waɗannan laifukan.
Hotunan tauraron dan adam sun nuna kaburbura da yawa a yankin.
Muna aiki tare da al'ummomi daban-daban don tattara bayanai da shaidu; ƙungiyoyinmu da abokan hulɗarmu sun ba mu bidiyo da shaidu da yawa.
Hotunan da muke da su suna da ban tsoro ƙwarai.
Your Comment