Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Firayim Ministan Isra'ila ta hanyar sanar da adawa a hukumance ga shirin shugaban Amurka na gudanar da shugabancin zirin Gaza wanda hakan kamar yadda a cewar kafofin watsa labarai na Ibrananci, alama ce ta rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.
Ofishin Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa inda ya yi watsi da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na kafa kwamitin kula da zirin Gaza, yana mai jaddada cewa matakin bai daidai da siyasar Tel Aviv ba kuma ya saba wa manufofin gwamnatin kasar. a cikin wata sanarwar da ofishin Netanyaho ya fitar ya zao cewa: "Ba a wani tuntube mu ba game da kafa hukumar gudanarwa da ke da alaƙa da abin da ake kira 'majalisar zaman lafiya,' kuma muna la'akari da wannan batu sabanin manufofin Isra'ila".
A cewar sanarwar, Netanyahu ya umurci ministan harkokin wajen Isra'ila Gadao Saer da ya mika sakon matsayin gwamnatin kasar Isra’ila zuwa ga sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio.
Your Comment