20 Disamba 2025 - 19:02
Source: ABNA24
Yadda Amerika Da Jordan Su Kai Tarayya A Hare-Haren Kan Syria

Rundunar sojin Jordan ta sanar da shigarta kai tsaye da rundunar sojin samanta a cikin wani aikin hadin gwiwa da Amurka kan abin da ta kira "wuraren ISIS" a kudancin Syria. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar Washington, an gudanar da aikin ne a cikin tsarin kawancen kasa da kasa da nufin hana farfado da ISIS.

Sanarwar rundunar sojin Jordan ta ce: A safiyar Juma'a, jiragen yakin kasar sun kai hare-hare ta sama kan wasu wurare da ISIS ke kai hari daga wajen a kudancin Syria.

Rundunar sojin Jordan ta jaddada cewa an gudanar da aikin ne da cikakken hadin gwiwa da Amurka da kuma cikin tsarin kawancen kasa da kasa kan ISIS; kawancen da gwamnatin Syria ta shiga cikinsa a kwanan nan.

A daren jiya, a matsayin martani ga kisan da ISIS ta yi wa sojojinsu biyu, sojojin Amurka sun jefa bama-bamai kusan 100 a kan wurare 70 na ISIS a Siriya ta amfani da jiragen yaƙi na F-15 da A-10 da kuma tsarin makamai masu linzami na Hymars.
A halin yanzu, an fitar da wani hoto da ke nuna ɗaya daga cikin sojojin Amurka yana rubuta sunayen sojojin biyu da aka kashe a kan bama-baman, wani abu da ke nuna martani ga harin ta'addanci na makon da ya gabata.

Your Comment

You are replying to: .
captcha