11 Nuwamba 2025 - 21:22
Source: ABNA24
IRGC: Ta Bankaɗo Tare Da Rusa Cibiyar Ƙungiyar Leƙen Asirin Amurka Da Isra'ila

Wannan muna sanar da mutanen Iran masu daraja cewa, ta hanyar matakan da Ƙungiyar Leƙen Asiri ta Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin ta ɗauka, an gano wata cibiyar tsaro da jami'an leƙen Asiri na Amurka da Isra'ila ke jagoranta a cikin ƙasar an kuma wargaza ta bayan wasu lokutan sa ido, bibiya, da sauran matakan leƙen Asiri.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jami'an sun kara da cewa: tsarin Sihiyona, a matsayin rundunar wakilcin Amurka a yankin, bayan gazawarta a Yaƙin Kwanaki 12, ta sauya manufofi da tsare-tsarenta zuwa ga wargaza tsaron jama'a don ta iya rama shan kayen da ta sha a fagen soja.

Dangane da wannan batu, wannan gwamnatin ta ƙirƙiri hanyar sadarwa ta hanyar mutane da aka yaudara masu cin amanar ƙasa don wargaza tsaron ƙasar a rabin ƙarshe na kakar 1404. Tare da taimakon Allah da kuma sa ido tsaro dakarun Imamuz zama na dakarun Leƙen Asiri ta Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin, an na yiwa membobin wannan cibiyar sadarwa kawanya kuma an kama su.

An gudanar da wannan aikin ne ta hanyar da ta dace a larduna da dama, inda aka kai hari kan wasu ƙungiyoyin da ke da alaƙa da gwamnatin Sihiyonawa waɗanda ke neman aiwatar da ayyukan da ke kawo cikas ga tsaro.

Your Comment

You are replying to: .
captcha