Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gidan yarin da ke cikin hamadar Negev da kan iyakar Masar, an dade ana kiransa da gidan yari inda ake gallazawa fursunonin Palasdinawa bisa ga salo salo na azabtarwa.
Itamar Ben-Gvir Memba na Ma'aikatar Tsaro ta Knesset ta Isra'ila ya fusata kan yunkurin da Tel Aviv ta yi game da masu fafutuka na Global Sumud inda
Ben-Gvir, jami'in majalisar ministocin yahudawan sahyoniya yaje gidan yarin da ake tsare da ayarin jiragen ruwan Sumud din. Bayan zuwansa ya ce: mun ɗauki Waɗannan mutane kamar 'yan ta'adda ne!
Itamar Ben-Gvir, ministan tsaron cikin gida kuma mai tsaurin ra'ayi a majalisar ministocin gwamnatin Sahayoniya, ya kira matakin da Tel Aviv ta dauka na mayar da 'yan fafutuka na Global Sumud da aka tsare zuwa kasashensuwani lamari mai cike da "damuwa da kuskure".
Ba tare da yin magana kan ta'addancin kasar Isra'ila ba, ya kira masu goyon bayan al'ummar Gaza "magoya bayan ta'addanci" ya kuma yi ikirarin cewa matakin da Netanyahu ya dauka na barin su komawa "kuskure ne babba." Ben-Gvir ya kara da cewa yakamata a tsare wadannan mutanen a gidan yari na tsawon watanni da dama kuma mayar da su zai ba da damar komawa kasar Falasdinu da Isra'ila tamamaye.
Your Comment